Firai Ministan Libya ya sha da kyar

Yan tawayen Libya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yan tawayen Libya

Firai Ministan kasar Libiya wanda kasashen duniya suka yarda da gwamnatinsa Abdullah al-Thinni, ya tsallake wani hari ba tare da samun ko kwarzane ba a lokacin da wasu da ke kokarin kashe shi suka yi wa motarsa ruwan harsasai a birnin Tobrouk na gabashin kasar.

Wani mai magana da yawun gwamnatin Libyar ya ce maharan sun bude wa Firaie Ministan wuta a lokacin da ya fito daga wani zama na majalisar dokoki.

An raunata daya daga cikin masu tsaron lafiyarsa.

A lokacin da ya yi magana da wani gidan Talabijin na Larabci al-Arabiyya bayan kura ta lafa -- Mr al_thinni ya ce "Ina godiya ga Allah, da muka tsallake wannan hari."

Karin bayani