'Mata 'yan kunar bakin wake na karuwa a Nigeria'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana amfani da yara mata wurin kunar bakin wake a Najeriya.

Hukumar kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya watau UNICEF, ta ce an samu karuwar 'yan mata da manyan mata masu kunar bakin wake a arewacin Nigeria.

Kungiyar ta ce cikin watanni biyar da suka wuce, an yi hasarar rayukan mata da yara 27 ta hanyar kunar bakin wake a wannan shekarar,fiye da shekara ta 2014.

Cikinsu akwai kananan yara da basu wuci shekara bakwai ba in ji UNICEF din.

UNICEF ta ce yawancin matan basu san abin da suke yi ba.

A cewar hukumar, 'yan tayar da kayar baya da gangar suke amfani da irin wadannan 'yan matan saboda zai yi wuya a bincike su in sun zo shiga kasuwanni ko tashoshin mota.