Harin sama ya hallaka 'yan gida daya a Yemen

Hakkin mallakar hoto
Image caption Ana ci gaba da fada tsakanin mayakan Houthi da gwamnatin Yaman

Wani harin sama na rundunar hadin gwiwar soji da Saudi Arebiya ke jagoranta a kasar Yaman ya hallaka wasu iyalai bakwai 'yan gida guda da suka hada da kananan yara biyu.

Harin ya fada kan gidan nasu da tsakar dare a yankin arewacin kasar ta Yaman, inda ke karkashin ikon 'yan tawayen Houthi.

Kazalika wani mutum guda kuma ya rasa ransa a wasu hare-hare da aka kai da makamai masu linzami, wanda ake zargin mayakan Houthi ne suka kai kan birnin Najran na kasar Saudiyya.

Wasu rahotanni kuma sun ce mayaka masu goyon bayan gwamnati sun fatattaki dakarun Houthi daga birnin Dalea.