Boko Haram: An kashe mutane 37 a Gubiyo

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau

Bayanai na baya-bayan nan da ke fitowa daga garin Gubiyo a jihar Borno na cewa mutane 37 ne suka mutu sakamakon harin da mayakan Boko Haram suka kai a karshen makon da ya gabata.

'Yan kato da gora na civilian JTF ne suka shaida wa gwamnan jihar Borno Alhaji Kashim Shettima hakan, yayin da ya ziyarci garin a ranar Talata domin ganin irin barnar da 'yan Boko Haram din suka yi.

Shugaban kungiyar 'yan kato da gora Bukar Mondama, ya shaida wa manema labarai cewa, mayakan na Boko Haram sun kuma kona gine-gine a kalla 400 da suka hada da masallatai takwas da makarantu hudu.

"Shammata"

Bukar Mondama ya kara da cewa mayakan na Boko Haram sun shammaci 'yan kato da gorar ne suka kaddamar da harin a lokacin da suke filin kwallo suna wasa.

'Yan Boko Haram da dama ne suka kutsa garin Gubiyo mai nisan kilomita 95 daga Maiduguri a kan babura da motoci a ranar Asabar da daddare.

Gwamna Shettima ya yi alkawarin bayar da diyya ga wadanda al'amarin ya shafa, tare da sake gina musu gidajensu da makarantu.

"Ku kara yin hakuri, wadannan mutane ba zasu taba yin nasara a kanmu ba. Mu ne za mu yi nasara a kansu," in ji gwamna Shettima.