Boko Haram : An damke mutane 643 a Niger

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Issoufou a zanga-zangar yaki da Boko Haram

Gwamnatin Niger ta tsare mutane fiye da 643 tun daga watan Fabarairun bana bisa zargin alaka da kungiyar Boko Haram.

Ministan tsaron Niger, Hassoumi Massaoudou shi ne ya bayyana haka a jawabinsa ga majalisar dokokin kasar, ya kara da cewar wadanda aka tsare din ana zarginsu ne da ta'addanci da hada baki wajen aikata miyagun laifuka.

Massaoudou ya ce gwamnatinsu ta zage damtse a yunkurinta na murkushe ayyukan Boko Haram.

"Idan ba mu dauki wannan matakin ba, to da rikici ya dabaibaye yankin Diffa," in ji ministan.

Tuni dai majalisar dokokin kasar ta amince da bukatar gwamnati ta tsawaita dokar ta-baci a jihar Diffa ta tsawon watanni uku.

Nigeria ta tura dakaru 3,000 a rundunar hadin gwiwa da aka kafa tare da Chadi da Kamaru da kuma Nigeria a wani matakin yaki da Boko Haram.