Tambuwal ya sauka daga kujerarsa

Hakkin mallakar hoto aliyu
Image caption Sai a watan Yuni za a rantsar da sabon shugaban majalisa

Shugaban majalisar dokokin Nigeria Aminu Waziri Tambuwal ya bar kujerarsa ta Kakakin majalisar gabanin karewar wa'adinsa a farkon watan gobe.

Tambuwal ya dauki wannan matakin ne domin samun damar shan ranstuwa a matsayin sabon gwamnan jiharsa ta Sakkwato da ake sa ran yi a ranar Juma'a.

Ya bar kujerar tasa ne a yayin wani zaman na bankwana da majalisar ta yi a ranar Laraba.

Can ma a fadar shugaban kasar, majalisar zartarwar kasar ta kamalla zamanta na karshe a karkashin Jagorancin shugaban kasar mai-barin-gado, Dr Goodluck Jonathan.

Majalisar dai ita ce mafi karfi a Najeriya, a tsarin mulki na shugaba mai ikon zartarwa.