Kalubale hudu da ke jiran Buhari

Hakkin mallakar hoto State House
Image caption Jonathan ya ce yana jin tsoron bita-da-kulli

Za a rantsar da Muhammadu Buhari a matsayin shugaban Nigeria a ranar Juma'a, amma kuma akwai kalulabe a gabansa wajen cika alkawuran da ya dauka a lokacin yakin neman zabe.

Ga wasu muhimman abubuwa hudu da zai tunkara da zarar ya dare kujerar mulki:

Cin hanci da rashawa:

Buhari ya ce cin hanci da karbar rashawa ba su da wuri a gwamnatinsa, abin da ya sa wasu ke tunanin zai yi irin ba-sani ba-sabon da ya yi a lokacin yana mulkin soja a shekarar 1984.

Hakkin mallakar hoto efcc website
Image caption Hukumar EFCC na da jan aiki a gabanta

Ya shaidawa shugaba mai barin gado Goodluck Jonathan cewar ka da ya ji tsaron komai ba zai masa bita-da-kulli ba.

Sai dai bangaren man fetur, wuri ne da Buhari ba zai iya kawar da kansa ba kuma ana bukatar garan-bawul domin rufe kofofin cuwa-cuwa.

Buhari ya yi alkawarin bayyana kaddarorinsa a matsayin wata hanyar yin komai a bayyane ba tare da muna-muna ba.

Tsaro:

Za a dinga tunawa da gwamnatin Jonathan kan karuwar ayyukan Boko Haram inda mutane kusan 15,000 suka mutu a yayin da wasu fiye da miliyan daya da rabi suka rasa muhallansu a cikin shekaru shida.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An kashe dakaru da dama a yaki da Boko Haram

Masana harkokin tsaro sun ce har yanzu akwai rina a kaba a yaki da Boko Haram, amma kasancewar Buhari tsohon soja ne ana ganin cewar yana da dabarun da zai kawar da masu tayar da kayar baya.

Sai dai yaki da Boko Haram na bukatar wasu shirye-shirye na bunkasa tattalin arziki da ayyukan yi tsakanin matasa.

Sannan akwai bukatar a ci gaba da hada kai da makwabtan kasashe kamar Chadi da Kamaru da kuma Nijar domin samun nasara.

Rashin aikin yi:

Kusan kashi biyu cikin uku na al'ummar Nigeria 'yan kasa da shekaru 30 ne. Amma rashin aikin yi ya kai kashi 30 cikin 100 duk da bunkasar tattalin arzikin da kasar ta samu a cikin 'yan shekarun nan.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Masu kananan sana'o'i na fuskantar tsaiko a Nigeria

Gwamnatin Buhari ta yi alkawarin bunkasa masana'antu da kuma gina layukan jirgin kasa, da hanyoyin mota da kuma ayyukan ci gaban kasa.

Masu sharhi sun ce Nigeria na bukatar ta sauya fasalin tattalin arzikinta domin rage dogaro da mai da kuma samar da ilimi ga kananan yara domin ci gaban kasar.

Makamashi:

A makon da ya gabata Nigeria ta ce tana samar da yawan wutar lantarki mai karfin megawatt 1,327 watau kasa da yadda ake samar da lantarki zamanin mulkin Buhari a shekarun 1983-1985.

Hakkin mallakar hoto
Image caption Rashin makamashi na ci wa 'yan Nigeria tuwo a kwarya

Ana sa ran Buhari ya yi garan bawul a fannin makamashi ta yadda za a samar da wadataccen lantarki ga 'yan Nigeria.

Dole ne kuma ya duba tsarin tallafin man fetur da gwamnati ke bayarwa, tsarin da ake tafka almudahana sosai a ciki.

Akwai kuma bukatar gyara matatun man fetur na kasar da kuma gina wasu sababbi domin magance matsalar karancin man fetur da ake yawan fuskanta a kasar.