A yau ake rantsar da sabon shugaban Nigeria Buhari

Hakkin mallakar hoto State House
Image caption Jonathan ya zagaya da Buhari a fadar Aso Rock

A yau ne a ke rantsar da sabon zababben shugaban Nigeria Muhammadu Buhari, a wani kasaitaccen buki da zai samu halartan baki daga ciki da wajen kasar.

A jiya Alhamis, shugaban kasar mai barin gado Goodluck Jonathan ya mika kundin bayanan mika mulki watau handover notes ga Muhammadu Buhari.

Kundin ya kunshi bayanan halin da Mr Jonathan zai bar wa sabuwar gwamnatin kasar da kuma irin harkokin da gwamnatin tarayya ke ciki.

Kafin mika kundin a yayin wani dan takaitaccen biki, Mr. Jonathan ya zagaya da Buhari a dukkanin sassan fadar ta Aso Rock domin nuna masa yadda gidan yake.

Can kuma a dandalin Eagles Square, an kayata dandali domin shirin bukin rantsar da sabuwar gwamnati a ranar Juma'a.

Inda za a rantsar da Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasa sai kuma Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin mataimakinsa.