An caccaki Suu Kyi a kan 'yan Rohingya

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Musulmi 'yan kabilar Rohingya na cikin mummunan yanayi

Jagoran addini a kasar Tibet, Dalai Lama ya bukaci wadda ta samu lambar yabon kyautata zaman lafiyar nan ta Nobel, Aung San Suu Kyi da ta kara himma wajen agaza wa al'ummar Rohingya a kasarta, wato Myanmar.

Ya ce a baya ma ya taba yin wannan magana da Ms Suu Kyi, kuma har yanzu yana cike da fatan za ta dauki mataki.

Ms Suu Kyi dai na shan caccaka da suka daga kasashen duniya cewa ta kasa cewa uffan game da halin takaicin da Rohinjawa suka samu kansu, kasancewar ba a amince da su a matsayin 'yan kasa ba a Myanmar.

Batun makomar Rihinjawan dai magana ce da ake kaffa-kaffa da ita a tsakanin al'umar kasar mabiya addinin Bhudda inda jam'iyyar siyasar Ms Suu Kyi za ta tsaya takara a wannan shekarar.

Wakilin BBC ya ce a watan Nuwamba ne za a yi babban zabe a Myanmar, kuma mutane da dama na fassara shirun da Ms Suu Kyi ta yi a matsayin taka-tsan-tsan irin na siyasa, saboda ta san cewa 'yan kasar Burma da dama sun ki-jinin Rohinjawa.