Wanene Muhammadu Buhari ?

Hakkin mallakar hoto APC Campaign Organistion
Image caption Buhari ya samu nasara bayan ya sha kaye sau uku a zaben Nigeria

Tsohon sojan, dogo, siriri, wanda aka haifa a garin Daura mai cike da tarihi da ke arewacin Nigeria, shekaru 72 da suka wuce.

Ya yi suna ne a shekarar 1983, a lokacin da ya hambarar da zababbiyar gwamnatin farar hulla.

A matsayinsa na soja mai mulkin kama-karya a lokacin, ya zama mutumin da ke nuna ba-sani-ba sabo wajen yaki da cin hanci da rashawa, inda ya kulle 'yan siyasa masu yawa da ake zargi da cin hanci da rashawa.

Tuni dai Muhammadu Buhari ya bayyana kansa cewar yanzu shima ya rungumi dimokuradiyya.

Ya samu nasara ne tare da gagarumin rinjaye a zaben da masu sa ido suka ce shi ne ya fi kowanne inganci wajen nuna adalci a kasar da ta fi kowacce karfin tattalin arziki a nahiyar Afrika.

Ya kuma samu wannan nasara ce, bayan da ya sha kaye a zabubbuka uku a baya.

'Mukamai'

Muhammadu Buhari, zai dare kan karagar mulki ne da dumbin gogewa a harkokin mulki, bisa la'akari da irin manya manyan mukaman da ya rike a gidan soja da kuma waje, wadanda suka hada da gwamnan, da ministan albarkatun mai da kuma uwa-uba shugabancin Nigeria karkashin mulkin soja.

Hakkin mallakar hoto RMA
Image caption Jonathan ya amsa shan kaye, inda ya kira Buhari a wayar salula

Buhari mutum ne da ya sha banban da sauran akasarin shugabannin Nigeria, saboda bai tara wata dumbin dukiya ba, duk kuwa da irin wadannan manya manyan mukamai da ya rage.

Akasarin jama'a a Nigeria sun yi shaidar sa a kan mutum mai rikon amana.

Zai karbi mulki ne a wani yanayi na tsuke bakin aljihu saboda faduwar farashin Mai da kuma raunin tattalin arziki wanda cin hanci da rashawa yayiwa katutu.

'Tsaro'

Babban kalubalen da ya fi bukatar sa ido, shi ne yakin tsawon shekaru shidan da Nigeria ke yi da kungiyar Boko Haram wadda ke da alaka da kungiyar IS a sashen arewa maso gabashin Nigeria.

Image caption Rikicin Boko Haram ya raba dubbai da muhallansu

Yakin dai ya yi sanadiyyar hallaka mutane fiye da dubu goma sha biyar, yayin da ya tagayyara wasu fiye da miliyan daya da rabi daga gidajensu.

Wannan dai shi ne zai kasance karo na biyu da za a rantsar da tsohon shugaban mulkin soja a Nigeria a matsayin shugaban farar hula, amma kuma shi ne karo na farko da za a mika mulki cikin ruwan sanyi daga hannun gwamnati mai ci zuwa ga hannun gwamnatin jam'iyyar adawa.