An rantsar da Buhari a matsayin shugaba

Hakkin mallakar hoto NTA
Image caption Tun a ranar Alhamis, Jonathan ya mika wa Buhari kundin bayanai

An rantsar da Muhammadu Buhari a matsayin sabon shugaban Nigeria a wani biki a Abuja.

Shugabannin kasashen duniya da dama ne suka halarci bikin wanda aka yi a dandalin Eagle Square.

Sannan an rantsar da mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo.

An kafa tarihi a karon farko a kasar inda dan adawa a dare kujerar mulki bayan da Mr Goodluck Jonathan ya amsa shan kaye a zaben da aka yi a watan Maris.

Wannan ne karo na biyu da Buhari zai karbi mulki, saboda a shekarar 1983 ya shugabanci kasar a gwamnatin mulkin soji.

Ya karbi mulki a lokacin da kasar ke fuskantar matsalolin tsaro da na tattalin arziki.