Za a bullo da sabbin dokokin intanet a Burtaniya

Hakkin mallakar hoto thinkstock
Image caption Allon shigar da haruffa a kwamfuta

Bullo da sabbin dokoki da zasu bai wa 'yan sanda da hukumomin leken asiri damar sa ido kan yadda mutane ke amfani da intanet a Burtaniya yana daga cikin jamabin Sarauniyar England.

Ofishin Firayiministan Burtaniya ya ce matakan wadanda suke cikin wani Kuduri na Ikon Bincike za su bai wa hukumomi damar kare jama'a.

Matakan za kuma su magance matsalolin da ake samu wajen tattara bayanan leken asiri da kuma damar da mutane suke da ita ta samun bayanai da ka iya zama barazana ga wasu.

Sai dai kungiyoyin masu kare hakkin dan'adam sun soki matakan, inda suka ce wata dama ce da za a rika yiwa mutane da yawa a Burtaniya leken asiri.

An tsara sabon kudurin ne ta yadda hukumomin leken asiri zasu samu damar sa ido sosai kan sadarwa ta intane, da sauran laifuka ta intanet.

Gwamnatin Burtaniya ta yi ta fuskantar matsin lamba a kan ta dauki mataki na dakile barazanar da kasar ke fuskanta ta intanet sakamakon ayyukan masu jihadi daga Iraki da Syria.