Hatsaniya a wurin rantsar da El-Rufai

Image caption Rufa'i ya maye gurbin Mukhtar Ramalan Yero

Rahotanni daga jihar Kaduna na nuna cewa an samu hatsaniya a dandalin Murtala Muhammed inda aka rantsar da sabon gwamna Malam Nasiru El-Rufa'i.

Bayanai sun ce jim kadan bayan rantsar da sabon gwamnan sai wasu matasa suka tayar da hargitsi suna jefar wasu manyan baki.

Wakilin BBC wanda al'amarin ya faru a gabansa, ya shaida mana cewa da kyar aka samu aka fitar da Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris ta kofar baya, sakamakon ruwan duwatsu da takalma da ake masa.

Ya kuma ce ya ga manyan mutane biyu wadanda aka ji wa rauni tare da wasu jami'an 'yan sanda.

'Yan sanda sun fesa hayaki mai sa hawaye a filin domin maido da doka da oda.

Kawo yanzu ba a san ko su wanene suka aikata lamarin ba.