Matasa 85 sun mika wuya a Kenya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta

Akalla mutane tamanin da biyar sun mika wuya ga gwamantin Kenya a inda suka yi musayar makamai sannan gwamnatin ta yi musu afuwa.

Matasan dai a baya suna bin akidar kungiyar 'yan tada kayar baya ta al-shabaab.

Gwmanatin Kenya ta bayyana mika wuyan na su a matsayin wani muhimmin abu saboda zai taimaka wajen tattaro bayanan sirri.

Jami'ai a ma'aikatar tsaro na cikin gida sun ce shekarun matasan bai wuce daga ashirin zuwa talatin ba.

Hukumomi sun sanar da afuwan a watan da ya gabata bayan da aka kai hari kan jami'ar da ke garin Garissa a arewa maso gabashin Kenya, inda a kashe kusan mutane 150.