Myanmar ta ce ceto 'yan ci-rani 700

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption 'Yan kabilar Rohingya na cikin mummunan yanayi a Myanmar

Kasar Myanmar ta ce sojin ruwanta sun ceto 'yan ci-rani fiye da dari bakwai a gabar ruwan kasar ta kudu.

Wani jami'in gwamnati ya ce mutanen sun hada da mata da kananan yara.

A ranar Juma'a ne wakilai daga kasashen yankin suka yi taro a birnin Bangkok na Thailand domin tunkarar matsalar.

Sun amince su kara kokartawa wajen ceto wadanda ke watangaririya a cikin teku da kuma tunkarar masu safarar mutane.

Sai dai Myanmar ta ki amincewa da wani jawabi na wani jami'in Majalisar Dinkin Duniya, cewa kamata ya yi ta yi wata dokar da za ta amince da Musulmin Rohingya a matsayin 'yan kasa.