Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Menene fatanku a kan Buhari?

Ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2015 rana ce mai cike da tarihi a Najeriya, domin a karo na farko tun bayan komawar kasar ga turbar dimokradiyya shekaru goma sha shida da suka wuce, mulki ya koma hannun jam'iyyar adawa ta APC.

Kuma wannan ne karo na farko a tarihin kasar da jam'iyyar adawa ta karbe mulki a hannun jam'iyya mai mulki.

Menene fatan ku akan sabon shugaban kasa, Muhammadu Buhari?