Barcelona ta lashe Copa del Rey

Image caption 'Yan wasan Barcelona suna murnar cin kofi

Barcelona ta dauki Copa del Rey, bayan da ta samu nasara a kan Athletic Bilbao da ci 3-1 a fafatawar da suka yi a Nou Camp.

Messi ne ya fara ci wa Barcelona kwallo, sannan kuma Neymar ya kara ta biyu kuma kwallo ta 38 da ya ci wa Barca a bana.

Bayan da aka dawo daga hutu ne Messi ya kara cin kwallo ta biyu a raga kuma ta 58 da ya ci jumalla a wasannin da ya yi wa Barca a bana.

Atletico Bilbao wacce ke da tarihin lashe copa del Rey sau 23 jumulla ta ci kwallonta ne ta hannun Williams saura minti 11 a tashi daga wasan.

Da wannan nasarar da Barcelona ta yi yasa ta dauki kofin karo na 27, kuma ita ce ta fi yawan lashe kofin a tarihi.

Barcelona wacce ke fatan lashe kofuna uku a bana, ta dauki kofin La liga Spaniya, za kuma ta buga wasan karshe a kofin zakarun Turai da Juventus a ranar 6 ga watan Yuni.