Rokokin Boko Haram sun kashe mutane 8

Hakkin mallakar hoto AP

A Najeriya mazauna birnin Maiduguri a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar sun ce akalla mutane takwas sun rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka samu raunuka a sakamakon farmakin 'yan Boko Haram.

Rahotanni sun ce mayakan Boko Haram sun harba rokoki ne zuwa birnin, wadanda suka fada a Unguwar Gomari da ke ketaren garin.

Mazauna wajen sun ce wasu irin manyan harsasai ne na kakkabo jiragen sama mayakan Boko Haram din suka rinka harbawa a lokacin da suka kasa kutsawa cikin garin na Maiduguri.

Sojojin Najeriya sun ce sun dakile kokarin da 'yan Boko Haram din suka yi na shiga birnin Maiduguri.

A ranar Juma'a ne sabon shugaban Najeriyar, Muhammadu Buhari, ya ci alwashin yin maganin 'yan Boko Haram.

Sakataren harkokin wajen Burtaniya, Philip Hammond, ya ce Burtaniya za ta taimaka wa sabon shugaban na Najeriya wajen bada cikakken horo ga jami'an tsaron kasar.

Yace: "Mun bukaci shugaban kasar ya sanar da mu jadawalin abin da yake bukata a duk lokacin da ya shirya.

"Wannan abu ne da jami'an tsaron Najeriyar za su tsara dangane da abin da suke bukata daga waje, musamman ta fannin sake inganta fasali da kuma horas da jami'an soji."

Karin bayani