Zabe: Erdogan ya nemi goyon bayan Musulmai

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban Turkiya, Recep Tayyib Erdogan

Shugaban Turkiya, Recep Tayyib Erdogan ya nemi goyon bayan musulmai masu ra'ayin mazan jiya a zaben 'yan majalisar dokokin kasar da za a gudanar nan da mako guda.

A wani jawabi daya gabatar na bukin tunawa da ranar kafa daular Othoman, Mista Erdogan ya sanya lamarin addini a gaba gaba, yana mai tabbatar wa Musulmai cewa za a ci gaba da kiran salla a kasar a fili.

Ya ce jam'iyyar sa ta AK wadda take da asali da addinin Musulunci, ba zata bin ra'ayin masu adawa da ci gaba da tasirin kafuwar daular Othoman tun a shekarar 1453.

Abokan hamayyar sa na ganin shawo kan masu ra'ayin 'yan mazan jiya da suka hada da Kurdawa akan su marawa jam'iyyar sa baya barazana ce ga demukradiyya.

Shugaban Turkiya na farko, Mustafa Kemal Ataturk shi ya soke aiki da tsarin musulunci a 1934, sannan ya daukaka al'adun turawa da suka hada da sanya tufafi da bai wa mata 'yanci.

Sai dai karfafa sha'anin addinin musulunci da Mista Erdogan ya yi, ya farfado da addinin a kasar.