Bam ya fashe cikin kasuwa a Maiduguri

Hakkin mallakar hoto AP

Wani bam ya fashe a birnin Maiduguri da ke arewa maso gabashin Najeriya, kuma mutane da dama sun samu raunuka.

Mazauna garin sun ce bam din ya tashi ne a Kasuwar Gamboru da ke kusa da ofishin kwastam a birnin.

Wannan ya zo ne kwana daya bayan wani dan kunar bakin wake ya tada bam a cikin masallaci a Maidugurin ya kashe akalla mutane 26.

Ana alakanta hare-haren ne da 'yan Boko Haram, wadanda a ranar Juma'a da daddare ma suka harba rokoki zuwa garin suka kashe akalla mutane takwas.

Sabon shugaban Najeriyar dai, Muhammadu Buhari, ya yi alkawalin magance rikicin Boko Haram.

A cikin wata sanarwar da ofishin yada labaransa ya bayar a ranar Asabar, Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa za ta yi amfani da karfin ikon da take da shi wajen murkushe abin da ya kira 'ta'addanci'.

Karin bayani