Buhari na shirin nade- naden mukamai

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jama'a sun zura idanu domin ganin irin mutanen da za'a nada mukamai a sabuwar gwamnati

Bayan rantsar da Muhammadu Buhari a matsayin sabon zababben shugaban kasar Najeriya, tuni 'yan kasar da dama suka kagara su ji sunayen wasu daga cikin shika shikan sabuwar gwamnatin.

Wani jigo a jam'iyyar APC mai mulki a Nigeria Sanata Lawal Shu'aibu ya shaidawa BBC cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya na nan yana shirin nade- naden mukamai

'Amma ya na da kyau a ba shi lokaci, watakila yau ko gobe litinin' in ji Sanata Lawal Shu'aibu.

Sanata Shu'aibu ya kara da cewa 'mukaman sun banbanta, akwai mukaman da sai 'yan majalisa sun amince da su, sannan akwai mukaman da Shugaban Kasa ya ke da damar yi kai tsaye.

Masu lura da al'amura dai na ganin cewa dole ne Shugaban Kasar ya zabo mutane na gari domin samun damar cika alkawuran da ya dauka.