Direbobi suna yajin aiki a Ghana

Image caption Accra, babban birnin Ghana

Direbobin motocin haya suna yajin aiki a Accra, babban birnin Ghana a wani zanga-zanga domin nuna adawa ga sabobbin dokokin da aka bullo da su.

Hukumomin kasar sun kirkiri wata doka inda suka ce sai masu takardar shaidar kammala karantun sakandare za a baiwa lasisin tukin mota.

Daya daga cikin dokokin shi ne na cewar direbobi su tabbatar sun daura bel na kujerar mota.

An soma yajin aikin a ranar Litini kuma ya saka mutane sun shiga cikin matsanancin hali.

Bayanai sun ce mutane a Accra na tafiya da kafa zuwa wurare masu nisa saboda rashin motocin haya.