Brazil ta lallasa Najeriya da ci 4-2

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin Najeriya, Steven Keshi

A gasar cin kofin duniya ta 'yan kasa da shekaru 20 da ake fafatawa a filin wasa na Yarrow dake New Plymounth, a kasar New Zealand, Brazil dai ta bude fagen ne da fara lallasa Najeriya da ci 4 da 2.

A mintuna 4 da fara wasa, Gabriel Jesus ya jefa kwallon farko sa'anan Isaac ya farke wa Najeriya a minti 10 da fara wasan.

Yahaya ne ya jefa kwallo ta 2, daga nan ne kuma Judivan ya farke sa'anan kuma Boschia ya jefa ta 3n, Judivan ya sake jefa kwallo ta 4n.

A ranar alhamis ne ake sa ran Najeriya za ta sake fafatawa a wasanta na gaba inda za ta kara da Korea ta Arewa.