Boko Haram: Buhari zai kai ziyara Nijar

Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari zai kai ziyara Jamhuriyar Nijar ranar Laraba, a wani mataki na kawo karshen hare-haren mayakan kungiyar Boko Haram.

Wannan dai ita ce ziyara ta farko da shugaba Muhammadu Buhari zai yi zuwa kasar waje kasa da mako guda da karbar ikon mulkin kasar.

Ziyarar na zuwa ne 'yan kwanaki bayan tashin bama-bamai da wasu sabbin hare-haren da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai a birnin Maiduguri da kuma wasu garuruwa na jihar Yobe, a arewa maso gabashin kasar.

Jim kadan dai bayan shan rantsuwar aiki, Muhammad Buhari ya yi wa 'yan kasar alkawarin kawo karshen mayakan Boko Haram, a inda ya ambaci hadin gwiwa da kasashe masu makwabtaka da suka hada da Nijar da Chadi da kuma Kamaru.