An hana shan taba cikin jama'a a China

Image caption Martin Patience ya gwada yanayin shan taba kafin a kafa dokar, tsakanin jama'a a Beijing.

An gabatar da wata sabuwar doka ta hana shan taba sigari a cikin jama'a a Beijing babban birnin China.

Akwai mashayan taba sama da miliyan 300, kuma mutane fiye da miliyan daya ne suke mutuwa sanadiyyar cututtuka da shan taba ke janyowa a kasar China a duk shekara.

An haramta shan taba a cikin jama'a dama a China, amma duk da haka an gaza tsaida ala'adar.

Haramta shan taba a wuraren cin abinci da wuraren aiki da kuma cikin motar haya na cikin tsauraran matakan da jami'an tsaro suka dauka domin hana shan taba cikin jama'a a Beijing.

Masana: Martin Patience, Labaran BBC, Beijing

Shan taba a China wani abin shakatawa ne ga kasar.

China ce take zukar kashi uku cikin 100 a tabar duniya.

Fiye da rabin kason maza a China mashaya taba ne.

Yawancin mutane sun fi ganin taba ta kamaci maza ne ba mata ba, domin haka da wuya a ga macce na shan taba.

Gaisuwar da ta fi inganci ita ce a miko taba, wacce ta fi tsada.

Kwalin sigari ita ce kyauta mafi inganci.

Masu yakin haramta taba sun ce yawancin mashayan taba ba su san illar ta ga lafiyarsu ba.

Akwai alamu cewa gwamnati ta sauya ra'ayinta.

Da wuya cikin shugabannin China a baya, kamar Mao da wanda ya gaje shi Deng Xiaoping a gan su ba tare da taba a hannu ba.

Amma shugaban China na yanzu ya kyamaci al'adar, ya kuma haramtawa jami'ansa shan taba cikin jama'a domin a yi koyi da su.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kudin kwalin sigari bai kai 5 yuan (kudin China) ba, watau dala 0.70.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mutane sama da miliyan daya sun rasa rayukansu sanadiyyar cututtukar da ta dangana da gubar hayakin taba a duk shekara.

"Suna da kunyatawa"

Ma'aikatar lafiya ta wallafa wuraren da aka haramta shan taba cikin jama'a da suka hada da Otal da kuma wuraren cin abinci a shekarar 2011.

Majalisar dokokin China ta sa hukuncin tarar 200 yuan (kudin China) watau dala 32 ga duk wanda ya saba dokar.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Akwai mashayan sigari sama da miliyan 300 a China, kuma ta zama abin sabon yau da kullum.

Hukuma Lafiya ta Duniya watau WHO ta yi maraba da wadannan tsattsauran matakai da aka dauka.

"idan an aiwatar da wannan doka, za ta kawo tsaftatacciyar iska a wuraren shakatawa a Beijing, hakan kuma zai kare mazauna Beijing fiye da miliyan 20 daga iskar taba mai guba." In ji wakilin WHO a China, Dr. Bernhard Schwartlander.

Duk da haka, akwai wadanda suke ganin tsananin farin jinin da al'adar shan taba ta ke da shi, zai iya hana dokar ta yi aiki.

Yang Gonghuan, tsohon mataimakin darektan Cibiyar kula da Cututtuka, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, "A gaskiya ba za a iya hana shan taba cikin jama'a ba, tun da mutane da dama mashayan taba ne."

Hakkin mallakar hoto Josephine Mcdermott
Image caption Wasu mata da miji a birnin Shanghai, sun cin abinci suna shan taba a cikin jama'a.

Dokar kuma ta hana tallan taba a kasar baki daya.