Bam ya kashe sojoji talatin takwas a Iraqi

Birnin Ramadi na kasar Iraqi Hakkin mallakar hoto
Image caption Birnin Ramadi na kasar Iraqi

Sojoji talatin da takwas ne suka halaka a Iraki a wani harin kunar bakin wake da mayakan IS masu da'awar kafa kasar musulunci suka kai.

Wata mota mai sulke ce aka cika makil da nakiyoyi, aka kuma kai karo da ita a kan wani sansanin 'yan sanda a birnin Ramadi.

Wani rahoto ya ce an kai wasu na cewa ba a dade da kai makamai masu lizzami ba zuwa wajen, kuma akwai Iraniyawa goma sha biyar a cikin sojojin da suka mutun.

A fili ne sojin Iran take goyon bayan sojin Iraki a fafatawar da suke yi da kungiyar IS.