An kashe jami'an tsaro 38 a Iraki

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kungiyar IS sun kai hari Ramadi

Akalla jami'an tsaro a Iraki 38 ne suka mutu a wani harin kunar bakin wake da kungiyar IS mai da'awar kafa daular musulunci ta kai.

Maharan sun kutsa motocinsu wanda aka cika da boma-bomai a wani sansanin soji da ke gabashin birnin Ramadi.

Wani rahoto ya bayyana cewar harin na farko ya haddasa wani fashewa a wani wurin ajiye makamai.

An sha fafata yaki a wannan yankin, yayin da dakarun gwamnati ke kokarin kwato wuraren da 'yan tawayen suka kama a baya-baya nan.

Kungiyar IS na tayar da kayar baya a kasashen Iraki da Syria lamarin da ya janyo mutuwar dubban mutane.