'Yan IS sun kashe sojan Iraki 38

Hakkin mallakar hoto

Akalla sojoji talatin da takwas ne suka halaka a Iraki a wani harin kunar bakin wake da ƙungiyar mayaƙan IS suka kai.

Wata mota mai sulke ce aka cika makil da nakiyoyi, aka kuma kai karo da ita a kan wani sansanin 'yan sanda a birnin Ramadi.

Wakilin BBC ya ce ba a dade da kai makamai masu linzami ba zuwa wajen, kuma akwai Iraniyawa goma sha biyar a cikin sojojin da suka mutun.

Iran tana taimakawa gwamnatin Iraki a yaƙin da take yi da 'yan ƙungiyar IS.