Zaki ya kashe wata mata a Afrika ta Kudu

Hakkin mallakar hoto TAUANA FILMS
Image caption Turawa na yawan zuwa yawon bude a gandun daji

Zaki ya hallaka wata Ba'amurkiya 'yar yawon bude ido a Afrika ta Kudu.

Manajan wurin yawon bude idon a Johannesburg, Scott Simpson ya shaida wa BBC cewa zakin ya shiga motar ne ta tagar da aka bari a bude sannan ya kashe matar.

Jami'an kiwon lafiya sun yi kokarin ceton lafiyarta amma sai ta ce ga garinku.

Mutumin da suke tare ya samu raunuka a kokarinsa na korar Zakin.

Manajan gandun dajin ya ce bisa dokar wurin an haramta yawo da mota da taga a bude a cikin gandun dajin.