Ana gab da samun maganin cutar daji ta huhu

Cutar daji ko Kansa Hakkin mallakar hoto SPL
Image caption Cutar daji ko Kansa

Wani gwaji da aka yi na wani maganin cutar daji watau kansa, ya nuna cewa ana gab da cimma nasarar samar da maganin cutar ta huhu.

Maganin "nivolumab" yana da tsaida yaduwar kwayoyin cutar dake boye ma garkuwar jiki, wanda ke sanya cutar yin illa ga bil-adama.

Sakamakon gwajin da aka yi a kan mutane 582 wanda aka gabatar ma kungiyar likitoci masana cutar daji ta Amurka, an bayyana shi da cewar, abu ne mai karfafa gwiwa ga majiyyata cutar.

Cutar dajin ta huhu, ita ce mafi hadari dake hallaka mutane, inda take hallaka kimanin mutane miliyan 1.6 a kowacce shekara.

Tana da wuyar sha'ani, saboda yawancin maganin ta bayan ta ci karfin masu fama da ita ake farga kuma mutanen dake fama da cututtuka masu nasaba da shan-taba sigari - ba su dacewa da tiyata.

Ana tsara garkuwar jiki ta yi yaki da cutar, to amma duk da haka tana kai ma sauran sassa hari idan har ba su yi aiki yadda ya dace ba kamar a kan cutar daji.

Sai dai kuma cutar mai karuwa, tana neman 'yan hanya ne kawai ta dore.

Irin wannan cutar dajin ta kan fitar da wani sinadari da ake kira PD-L1 wanda ke dakatar da duk wani tsari na garkuwar jiki wanda ya nemi kai ma ta hari.

Wannan sabon magani da aka gano da ake kira "Nivolumab" yana daya daga cikin jerin magungunan da ake kira magunguna masu binciken garkuwar jiki wanda kamfanonin magunguna suka harhada.

Ya kan tsayar da cutar dajin daga hana dakatar da tsarin garkuwar jiki, ta yadda za ta cigaba da kai hari kan cutar daji, ta kashe ta.

Karin bayani