Senegal ta haramta amfani da jakar leda

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yadda ake zubar da ledoji barkatai

Senegal ta zamo kasa ta baya-bayan nan da ta haramta amfani da jakar leda a nahiyar Afrika domin kare muhalli.

Ta bi sahun kasashe irin su Kamaru da Kenya da Tanzaniya da Uganda da kuma Murtaniya inda hukumomi suka kimanta cewa kashi 70 cikin 100 na shanu da tumaki da ke mutuwa a Nouackchott babban birnin Murtaniya, na mutuwa ne sakamakon cin ledoji da ake zubarwa barkatai.

Masu kananan sana'i'o suna korafin cewar ba su san yadda za su ci gaba da kasuwancinsu ba tare da amfani da ledojin ba.

Sun ce haramta amfani da ledojin zai zamo kawo babban nakasu a sana'arsu, domin suna amfani da su wajen zuba wa abokan ciniki kayan da suke sayarwa kamar su nama da kayan marmari da kuma kayan miya.