Kawunan Sanatocin Amurka sun rabu

Majalisar dattawan Amurka Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Majalisar dattawan Amurka

Wa'adin da aka tsayar a Amurka na sabunta dokokin yaki da ta'addanci ya kare bayan majalisar dattawan ta gaza sabunta dokokin.

Wannan ne dai zai bai wa hukumar kula da sha'anin tsaron kasa damar tattaro bayanai na wayoyin tarho na 'yan kasar ta Amurka.

Bangarorin da suka gaza samun jituwa a cikin 'yan majalisar dattawan na jam'iyyar Republican sun gaza daidaitawa.

Fadar gwamnatin Amurka ta bayyana cewa hakan wani koma-baya ne da bai dace ba, tana kira ga 'yan majalisar dattawan su jingine bambancin ra'ayin siyasa su gaggauta gyara al'amurran.

Karin bayani