Buhari na son nada mashawarta 15

Hakkin mallakar hoto senate website
Image caption Shugaban majalisar dattijai Sanata David Mark

Shugaba Muhammadu Buhari ya aika takarda zuwa majalisar dattijai domin neman amincewarta ya nada mukaman mataimaka na musamman 15 a gwamnatinsa.

Shugaban majalisar dattijai, Sanata David Mark ne ya karanta takardar a zauren majalisar a ranar Talata.

Amma takardar ba ta bayyana sunayen wadanda za a bai wa mukaman ba.

Takardar dai ita ce ta farko daga shugaba Buhari zuwa ga majalisar dattijan tun bayan da aka rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu.

Tun a ranar Lahadi, Shugaba Buhari ya nada masu magana da yawunsa watau Femi Adesina da kuma Garba Shehu.