Buhari na tattaunawa da jami'an tsaro

Hakkin mallakar hoto State House
Image caption Shugaba Muhammadu Buhari ya sha alwashin murkushe Boko Haram

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya na can yana wata ganawar sirri da dukkan manyan jami'an tsaron kasar a ofishinsa na wucin-gadi da ke birnin kasar.

Taron dai na zuwa kwana daya kafin shugaban ya kai wata ziyarar aiki a makwabtan kasashen Nijar da Chadi inda ake sa ran ya tattauna da shugabannin kasashen kan yadda za su murkushe kungiyar Boko Haram.

Masu halartar taron dai sun hada da Babban hafsoshin kasar, da shugabannin rundunoni sojojin kasa da sama da kuma ruwa.

Haka ma akwai mai ba Shugaban kasa shawara kan lamurran tsaro da Babban sufetan 'yansandan kasar da sauransu.