Jirgin ruwa ya nutse da mutane a China

Jirgin ruwa Hakkin mallakar hoto
Image caption Jirgin ruwa

A ranar Litinin ne wani jirgin ruwa dauke da kimanin mutane 450 ya nutse a kogin Yangtze na kasar China, sakamakon matsanancin ruwan sama.

Kafofin watsa labarai na kasar sun bayar da rahoton cewa an ceto mutane 20 da suka hada da matukin jirgin ruwan da babban injiniyansa.

Daga cikin wadanda ma'aikatan ceto suka tsamo akwai wata mata 'yar kimanin shekaru 85.

Kazalika har yanzu ba a ji duriyar mafi rinjayen mutanen ba tun fiye da sa'oi 12 da nutsewar jirgin ruwan.

Karin bayani