Ashe mutum dama can dan ta'adda ne ?

Kokon kan mutumin da aka yi nazari
Image caption Kokon kan mutumin da aka yi nazar

Wata sheda ta nuna cewa mutanen da suka yi zamani shekaru tun 430,000 da suka wuce, suna tafka aika-aika.

Wasu gawarwaki da aka bincika daga cikin wani kogo a arewacin kasar Spain sun nuna cewa an yi ma wasu raunuka da nufin kashe su tun shekaru 430,000.

Masu binciken sun yi nazarin daya daga cikin kokon kan mutanen daga wani wuri da ake kira ramin kasusuwa wanda ya kunshi gawarwakin a kalla mutane 28.

Masanan sun yi ittifakin cewa wasu raunuka biyu da aka yi ma kokon kan ga alama mugun bugu ne wanda ya nuna an ayyana kisa ne.

An buga sakamakon binciken a mujallar PLOS One.

Tare da bayar da dalilan da suka sanya gawarwakin suke cikin wannan kogo, masana kimiyya sun ce nazari ya nuna shedar cewa, ta'addanci wani bangare ne na al'adun mutanen da.

Wata kungiyar masu bincike ta kasa da kasa, ta nazarci kokon kan da aka yi ma lakani cranium 17, ta hanyar amfani da wasu na'urori na kintace na masana kiwon lafiya na zamani.

Dukkansu dai sun yi amanna cewa, wata tsaga guda biyu da aka yi ma kokon kan a gaba wadda ta yi kama, babbar manuniya ce cewar an yi amfani da makami guda ne.

Jagoran masu binciken Dr Nohemi Sala daga Cibiyar Salud Carlos na 111 dake birnin Madrid ya gaya ma sashen labarai na BBC cewar "wannan mutumin da aka yi nazarin kokon kansa an kashe shi ne lokacinda suke fada da wani."

Wannan dai ya hasko wani abinda ba a da masaniya game da rayuwar kaka da kakanninmu.

Karin bayani