Under-20: Ghana ta doke Argentina 3-2

Yaw Yeboah
Image caption Ghana tana da maki 4 daga cikin wasanni biyu da ta yi a gasar

Tawagar kwallon kafar Ghana 'yan kasa da shekaru 20 ta doke ta Argentina da ci 3-2 a gasar cin kofin duniya ta matasa da suka kara a New Zealand.

Ghana ta ci kwallayenta uku ne ta hannun Benjamin Tetteh da Clifford Aboagye da Yaw Yeboah wanda ya ci da fenariti.

Argentina ta zare kwallaye biyun da aka zura mata ne a raga ta hannun Giovanni Simeone da kuma Emiliano Buendia.

Da wannan nasarar Ghana tana da maki hudu tare da Ausria wacce ta doke Panama da ci 2-1.

Ghana za ta yi wasan karshe na cikin rukuni da Panama a ranar Juma'a, yayin da Austria za ta fafata da Argentina.