Butum-butumi zai kula da otal a Japan

Mai yiwuwa kwana-kwanan nan butum-butumi zai maye gurbin mutane wajen tarbar baki a otal.

Image caption Butum-Butumin za su kasance 'yan mata masu kama daya

A watan Yuli ne dai za a bude wani otal mai suna Henn-na a birnin Sasebo na Japan, kuma masu otal din suna fatan zai zama wani zakaran gwajin dafi a harkar saukar baki.

Butum-butumi goma ne da kuma mutane biyu kacal za su rika aiki a harabar otal din.

Butum-butumin za su dinga gayar da baki da daukar musu jakunkuna; kai har ma da tsaftace dakunan kwanan baki da zarar bakin sun tafi.

An tsara butum-butumin, wadanda aka kera da fuska irin ta mata, ta yadda za su yi magana da harsuna daban-daban su kuma amsa tambayoyin baki a otal din mai dakunan kwana 72.

Hakkin mallakar hoto
Image caption Butum-butumi masu fuskar mata

Manufar otal din ita ce samar wa baki duk wani nishadi da ci gaban zamani zai iya bayarwa, ciki har da manhajar da za ta iya shaida fuskar mutum ta bude masa kofa.

Koda yake ba kowanne mai aikin otal ba ne yake fuskantar barazanar rasa aiki sakamakon amfani da butum-butumi, sai dai harkar otal na rungumar sababbin hanyoyin fasaha.