Al-Shabab ta kwace kauye a Kenya

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Dalibai 150 mayakan al-shabab suka kashe a Garissa

Mazauna kauyen Wankara da ke arewa-maso-gabashin Kenya sun ce mayakan al-Shabab sun kwace iko da kauyen.

Bayanai sun ce an rufe makarantu a yayin da daruruwan mutane suka tsere daga kauyen na Wankara.

Wannan ne karon farko da al-Shabab ta kwace iko da wani mazaunin jama'a a lardin Mandera da ke arewa maso gabashin kasar.

Gwamnatin Kenya ta tura dakarunta zuwa Somalia a shekara ta 2011 domin yaki da al-Shabab wacce ta kaddamar da hare-hare a wurare da dama a Kenyar.

A kwanakin baya mayakan al-Shabab sun hallaka dalibai kusan 150 a wani hari da suka kaddamar a kan jami'ar Garissa.