Agogon kece-raini na Aisha Buhari

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wannan hoton na matar shugaban Nigeria sanye da agogon da aka ce mai tsada ne ya bakanta ran 'yan kasar.

Hotunan Agogon kece-rainin da uwargidan shugaban Nigeria ta sanya sun sa wasu 'yan kasar su na tambaya kan ko hakan ya rage farin-jinin Muhammdu Buhari a tsakanin jama'a.

Hotunan matar shugaban kasar Nigeria sanye da wani agogo da aka ce mai tsada ne ya sa wasu 'yan Nigeria na tambaya a kan tasirin da hakan zai yi.

A cikin watan Maris aka zabi Muhammadu Buhari a matsayin shugaban Nigeria, bayan wani yakin neman zabe a kan cewar zai yi yaki da cin hanci da karbar rashawa.

Buhari ya nuna tawali'unsa a lokacin kamfe har ma talakawa suka ba da gudunmuwa a wajen yakin neman zabensa.

A cewarsa, ya karbi bashin banki kafin ya sayi fom din zama dan takarar jam'iyyarsa.

Sai dai kimarsa ta dan sauya, lokacin da aka ga matarsa, Aisha Buhari sanye da wani agogo da aka ce mai tsada ne sosai a lokacin bikin rantsar da mijinta a makon da ya gabata.

Wani mai daukar hoto, George Okoro ya wallafa hoton wannan agogon a shafinsa na Instagram.

'Farin Zinare'

Kafafen yada labarai a Nigeria sun ce agogon kirar 'Cartier Baignoire Folle' an yi masa kwalliya da farin zinare kuma an kiyasta kudinsa a matsayin kusan dala dubu 50 watau fiye da naira miliyan 10.

Amma wasu sun nuna wani agogon mai kama da wannan wanda ake sayarwa kusan dala 100 watau sama da naira dubu 20.

Nigeria dai ta yi kaurin suna wajen sayar da kayayyakin jabu da suka yi kama da masu tsada.

Sannan Aisha Buhari ta saka agogonne kafin mijinta ya zama shugaban Nigeria.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ana sayar da irin agogon Aisha Buhari a kan dubban daloli

A shafin Twitter an ambaci batun wannan agogon da matar shugaban Nigeriar ta sa sau kusan 3,000.

Wasu sun nuna ayar tambaya da kuma kushe Aisha Buhari a kan shin a ina ta samu kudin mallakar wannan agogo mai tsada?

"Aisha Buhari ta saka agogon naira miliyan 10 amma mijinta ya gaya mana cewar ya ranci kudi domin sayen takardar takarar shugaban kasa," in ji Kate Vincent a shafinta na Twitter.

Amma wasu sun kare ta inda suka ce "Aisha Buhari ba ta yi amfani da kudin Nigeria ba wajen sayen agogonta, shin ina ruwanku? Menene abin damuwa kai? in ji @SalaudeenNana.