An fadada bincike a kogin China

Jirgin ruwa na masu bincike a kogin Yangtse Hakkin mallakar hoto Xinhua
Image caption Jirgin ruwa na masu bincike a kogin Yangtse

Jami'ai a kasar China sun ce ba su yanke kauna ba a binciken da suke yi na samun masu sauran shan-ruwa, a jirgin ruwan nan da ya nutse bayan ma'aikatan ceto sun shafe dare na biyu suna binciken ko akwai sauran mutanen da hadarin ya rutsa da su a cikin jirgin.

Har yanzu dai babu duriyar mutane sama da 400.

Jami'ai sun ce an fadada binciken da ake yi a Kogin na Yantse zuwa karin sama da kilomita 150 a cikin ruwan.

Dubban 'yan sanda da ma'aikatan kwana-kwana da sojoji da ke binciken, suna fama da yanayi mai matukar muni saboda ruwan saman da ake shekawa da iska mai karfin gaske.

Karin bayani