Tsaftataccen makamashi maganin sauyin yanayi

Jirgin Sama mai amfani da haske Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jirgin Sama mai amfani da haske

Kungiyar wasu masana kimiyya da masana harkokin tattalin arziki sun yi kiran da a aiwatar da wani shiri kwatankwacin shirin nan na tura 'yan sama jannati sararin samaniya na Apollo, don samar da tsaftataccen makamashi kuma mai rahusa.

Shirin na Apollo ne ya sanya masana kimiyya tura 'yan sama jannati duniyar wata a lokacin yakin cacar baka.

Masanan suka ce ana bukatar wani yunkuri irin wannan wajen samar da makamashi mai rahusa fiye da amfani da gawayi a cikin shekaru goma a wani abinda suka kira babban kalubale na kimiyya na karni.

An sha bayar da irin wannan shawarar a can baya, to amma abin yana cin tura.

Kungiyar kwararrun ta kira wannan shiri, Apollo da zai game duniya.

Suka ce manyan kasashe da dama sun nuna sha'awar su ta shiga wannan shirin na saka wani bangare na kudaden shigar da suke samu a shekara wajen bincike da samar da tsaftataccen makamashin nan.

Rahoton na su wanda aka kaddamar a kungiyar nan ta masana ta London Royal, ya nuna cewar a tafiyar da ake yi yanzu, duniya za ta zarce ma'aunin shiga hadari na sauyin yanayi watau 2c zuwa shekara ta 2035.

Masanan suna karkashin jagorancin tsohon Babban masanin kimiyyar nan ne na Brittaniya Farfesa Sir David King.

Ya gaya ma sashen labarai na BBC cewar "mun rigaya mun gano hayakin da zai dumama duniya a lokutta da dama."

Abu daya ne kawai zai iya dakatar da mu daga fitar da shi - watau idan aka samar da makamashin da zai zamo mai rahusa fiye da na injuna masu aiki da mai da ake amfani da su.

Yace, "a karkashin shirin na mu, muna burin tabbatar da cewar hakan ya yiwu a duk fadin duniya cikin shekaru goma masu zuwa."

Karin bayani