An hana sayar da wata taliya a India

Image caption Taliyar Maggi Noodle

Hukumomi a Delhi, babban birnin India sun hana sayar da wata sananniyar taliya bayan da aka gano cewar ana samun dalma da yawa a cikin ta, bayan wani gwaji da aka yi a kan taliyar.

Delhi ita ce jihar da a baya-bayan nan ta sanar da cewar an samu burbudin dalma da yawa wanda zai iya cutarwa a cikin taliyar 'Maggi noodles' wanda kamfanin Nestle da ke India ke yin ta.

Sai dai kuma kamfanin ya kafe a kan cewar taliyar ba za ta cutar ba.

Taliyar Maggi Noodles sananniya ce ne a India.

Jarin kamfanin Nestle ya fadi da kashi goma cikin 100 tun da aka yi sanarwar farko a watan Mayu game da yawan dalmar da ke cikin Taliyar Maggi Noodle.