Habre ya bayyana gaban kuliya a Dakar

Hakkin mallakar hoto s
Image caption Hissene Habre

Tsohon shugaban Chadi, Hissene Habre, wanda ake tuhuma da laifin cin zarafin bil'adama, ya gurfana a gaban kotu a Dakar, babban birnin Senegal a karon farko.

Masu aiko da rahotonni sun ce tsohon shugaban, ya ki barin dakin sa a gidan yari sakamakon hakanne ya sa aka tirsasa shi aka fitar da shi aka gabatar da shi wurin alkali.

Ya ki ya amsa tamboyi da aka yi masa kuma lauyoyinsa sun ce kotun ba halattaciya ba ce a wurinsa.

An kusa a fara shari'ar da ake yi wa Hissene Habre inda ake tuhumarsa da azabtarwa da kuma laifukan yaki da kuma cin zarafin bil'adama a wata kuto ta musamman da take da goyon bayan tarayyar Afrika a Dakar a ranar 20 ga watan Yuli.

Kungiyar kare hakin bil'adama ta ce kusan mutane dubu arba'in aka kashe a lokacin da ya ke mulki a shekarar 1980.