'Sojojin Nigeria sun aikata laifukan yaki'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Air Marshal, Alex Badeh na daga cikin wadanda ake tuhuma a rahoton

Kungiyar Amnesty International ta ce ya kamata a tuhumi wasu manyan sojojin Nigeria da laifin cin zarafin bil'adama da kuma laifukan yaki.

A wani rahoto kan yaki da Boko Haram, kungiyar ta Amnesty ta ce a cikin shekaru hudu mutane fiye da 7,000 maza da kananan yara sun mutu a lokacin suna garkame a hannun sojoji.

Rahoton ya bayyana sunayen wasu manyan janar-janar da cewa ya kamata a bincikesu da laifin kisan kai da azabtar da jama'a da kuma batar da mutane.

Rahoton ya bayyana cewa sakamakon hare-haren Boko Haram a yankin arewa-maso-gabashin Nigeria an tsare matasa kusan 20,000.

Amnesty ta ce "A wasu lokuta da gayya ake barin mutane cikin matsananciyar yunwa kuma tun daga watan Maris na 2011 mutane 7,000 sun mutu a lokacin da suke zaman wakafi a wurin sojoji."

Kungiyar ta yi kira ga sabon shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari ya kawo karshen rashin bin doka a bangaren dakarun kasar.

A martanin da ta mayar rundunar tsaron Nigeria ta ce Amnesty na kokarin bata ma ta suna ne.