'Amnesty na kokarin ɓata mana suna'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Manjo Janar Chris Olukolade ya ce babu gaskiya a rahoton Amnesty

Rundunar tsaron Nigeria ta mai da martani cikin fushi game da rahoton da kungiyar Amnesty International ta fitar, inda ta zargi manyan jami'an sojin kasar da laifin kashe dubban matasa.

Kakakin rundunar, Chris Olukolade a cikin wata sanarwa ya zargi kungiyar kare hakkin bil'adama din da yunkurin ɓata sunan dakarun Nigeria.

A cewarsa, rundunar ba ta daure wa sojojinta gindi su aikata laifukan cin zarafin bil'adama.

Tun da farko, Amnesty ta bayyana sunayen wasu manyan kwamandojin sojin Nigeria da ta ce ya kamata a tuhumesu da aikata laifukan yaki.

A cewar Amnesty din, a cikin shekaru hudu mutane fiye da 7,000 maza da matasa sun mutu a lokacin suna garkame a hannun sojoji.

Amnesty ta ce "A wasu lokuta da gayya ake barin mutane cikin matsananciyar yunwa kuma tun daga watan Maris na 2011 mutane 7,000 sun mutu a lokacin da suke zaman wakafi a wurin sojoji."

Kungiyar ta yi kira ga sabon shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari ya kawo karshen rashin bin doka a bangaren dakarun kasar.