An kama mawaki a Senegal da kudin jabu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Thione Seck

Ana tuhumar wani shahraren mawaki dan Senegal da yin zamba bayanda aka gano dubban miliyoyin kudin Euro na jabu a gidansa.

Thione Seck wanda aka kuma tuhuma da laifin halatta kudin haram da kuma yin amfani da kudin jabu, ya bayyana a gaban masu shigar da kara a Dakar, babban birnin Senegal a ranar Talata.

Mawakin ya karyata laifin da ake tuhumarsa da shi, inda ya ce wani mai tallar shirin wasanni da ke kasar Gambiya ne ya ba shi kudaden a matsayin wani kaso na kudaden da za a biya shi na wani yawon shakatawa na duniya da za'a yi.

Thione Seck ya shafe shekaru da dama tauraronsa na haskakawa a matsayinsa na mawaki.

Seck ya samu kyautuka tare da wasu mawaka da ake kira Orchestra Baobab.