Ana zanga-zanga kan cin zarafin mata

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Zanga-zanga kan cin zarafin mata a Ajantina

Dubban mutane ne suka yi zanga-zanga a Bunis-Aris babban birnin Ajantina domin nuna adawa kan cin zarafi da keta haddin mata.

Zanga-zangar ta biyo bayan kashe-kashen mata da aka dinga yi a jere wadanda suka daga hankalin al'ummar kasar, ciki har da kisan wata Malamar makaranta wadda mijinta ya yi mata yankan rago a gaban dalibanta.

Kungiyoyin kwadago da jam'iyyun siyasa da cocin katolika sun nuna goyon bayansu ga masu zanga-zangar.

Gwamnatin Ajantina ta jima da sanya hannu kan wata doka da ke yaki da cin zarafin mata amma masu fafutuka sun ce ba a amfani da dokar yadda ya dace.

Haka ma, an gudanar da irin wannan zanga-zanga a kasashen Chile da Yurugwai da ke makwabtaka da Ajantina.