Fa'idar binciken sankarar nono

Binciken sankarar nono Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Binciken sankarar nono

Wata kungiyar masana kimiyya ta duniya ta tabbatarwa Mata cewar binciken sankarar nono ya kan taimaka wajen ceton rayukka.

Nazarin dai ya biyo bayan muhawarar da aka tufka ne a game da illa ko rashin illar dake tattare da hanyar binciken sankarar nonon.

A karkashin jagorancin reshen hukumar lafiya ta duniya dake kula da sankarar nono, kwararrun 29 daga kasashe dabam-dabam na duniya sun yi nazarin wasu jerin binciken da aka gudanar guda 40.

Sakamakon binciken na su da aka buga a mujallar magunguna ta Brittaniya ya goyi bayan shawarar da hukumar lafiya ta Brittaniya ke baiwa mata masu shekaru tsakanin 50 da 69 su rinka zuwa ana bincken nonon su a cikin kowadanne shekaru ukku.

To sai dai kuma adadin matan dake zuwa binciken a Brittaniya ya ragu cikin 'yan shekarun nan.

Rahoton yace duk da cigaban fasaha da aka samu, magungunan cutar sankarar nonon da damuwar da ake da ita a kan hadarin dake tattare da ita, binciken har yanzu yana ceton rayukka.

Hukumar lafiyar ta Brittaniya ta yi kiyasin cewa an ceci rayukkan mata 1,300 a shekara daga sakarar ta nono a Brittaniya.

To sai dai kuma duk da haka rahoton ya amsa cewar akwai hadurran dake tattare da hanyoyin binciken - kamar na bayar da maganin dake zarce kiima, wurinda za a gano wata sankarar nonon da ba ta taka kara ta karya ba wadda ba za ta ma yi wata illa ba, amma a wasu lokutta a bayar da maganin bai zama wajibi ba.

A wasu lokutta kuma ana cigaba da yi ma Mata karin gwaje-gwaje kafin a tabbatar cewa ba su da sankarar ta nono, saboda a wasu lokutta binciken ya kan gano wasu sauye-sauye wadanda ba sankarar ta nono ba ce.

Farfesa Stephen Duffy na Jami'ar Queen Mary dake London wanda ya shirya wannan rahoto ya ce, wannan nazari da aka yi, suna fata zai kara tabbatar ma Mata cewar a fadin duniya cewar binciken nono zai iya ceton rayukka.

Karin bayani