An dage zaben Burundi

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaban Burundi Pierre Nkurunziza mai son tazarce karo na uku

Hukumomi a kasar Burundi sun ce an dage zaben Shugaban kasa da na majalisar dokoki da aka shirya gudanar wa a cikin wannan watan, sakamakon watannin da aka shafe ana zanga-zanga.

Wani mai magana da yawun Shugaba Pierre Nkurunziza ya gaya wa BBC cewa nan ba da jimawa ba, hukumar zaben kasar za ta sanar da sabbin ranakun da za a gudanar da zaben.

Yunkurin dai ya biyo bayan rokon da Shugabannnin kasasahen gabashin Afrika suka yi ne a ranar Lahadin da ta gabata, na neman a jinkirta zaben da makonni shida.

Kasar ta Burundi dai ta tsunduma cikin rudani bayan da Shugaba Nkurunziza ya yi shelar fitowa takarar wani wa'adin mulkin na uku -- lamarin da ya haddasa yunkurin juyin mulkin da ba a yi nasara ba da kuma mummunar zanga-zanga kan tituna wadda ta yi sanadiyar mutuwar sama da mutane 30.